Yadda Ake Dauko Gawarwakin Mutum Goma Sha Biyar 15 Din Da Suka Nutse A Kogi

0

Tofa! Yadda Ake Dauko Gawarwakin Mutum Goma Sha Biyar 15 Din Da Suka Nutse A Kogin Maiduguri Innalilahi

Akalla gawarwakin mutum 15 aka gano a kogin Ngadabul a Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan afkuwar wata ambaliya.

Kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a arewa maso gabas, Muhammad Usman, shi ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Related Posts
1 of 407


Usman ya ce ana samun karuwar mutane da ke nutsewa cikin kogin sakamakon ambaliya wanda kuma ya shafi al’ummomi da ke kusa bakin kogin a Maiduguri.

Ya bukaci iyaye da su gargadi ‘ya’yansu kan yin ninkaya a kogin domin kaucewa nutsewa.

Kodinetan na NEMA ya kara da cewa hukumar ta samar da kayakin gagaji da za ta baiwa wadanda ambaliyar ta shafa inda kuma take wayar da kan al’umma kan haduran ambaliyar ruwa da kuma hanyoyi da za su kare kansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy