YADDA Wani Mahauci ya Dabawa Mahaifinsa Wuka

0

Tofa! Wani Mahauci ya dabawa mahaifinsa wuka lokacin da yake yin sallah a garin Zaria

Fitaccen dan bindiga da ya addabi yankunan jihar Zamfara Dogo Gide ya aure daya daga cikin daliban makarantar sakandare ta Yawuri da yai garkuwa dasu.

Sannan kuma ya aurar da wasu daga cikin daliban ga yaransa. Daliban dai su kimanin 90 da malamansu 11 ne aka yi garkuwa dasu tun tsawon shekara daya da rabi da ta gabata, a cewar rahoton shafin Hausa na RFI.

Related Posts
1 of 407


Tun bayan lokacin da aka yi garkuwa da matar daliban wasu daga ciki sun samu sun kubuta da kansu wasu kuma jami’an tsaro suka kubutar dasu inda har zuwa yanzu akwai daliban da yawa a hannun yan bindigar da basu tsira ba.

Wani mai magana da yawun iyayen yaran Salim Kaoje ya bayyana cewa sun samu labarin shugaban yan bindigar Dogo Gide ya auri daya daga cikin daliban ya kuma aurar da wasu ga yaransa kamar yadda ya shaidawa Jaridar Premium Times.

Ya ce Gide ya tabbatar musu cewa Idan har suna son a saki ragowar daliban dole sai an biya Naira Miliyan 100, idan kuma ba haka ba za su ci gaba da zama a hannun su.

Kawo yanzu dai an bayyana cewa daliban na Yawuri sun shafe kwanaki 554 a hannun yan ta’adda wanda ya haura shekara daya da rabi ba tare da sun sheki iskar yanci ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy