Yadda Wani Yaro Dan Shekaru 13 Ya Yiwa Uwar Sa Ciki

0

Turƙashi Yaro Dan shekaru 13 Ya Yiwa 'Yar Uwarsa 'Yar Shekara 9 Ciki Innalilahi

‘Yan sandan kasar Zimbabwe sun tabbatar da cewa wani yaro dan shekara 13 ya yi wa wata yar uwarsa mai shekaru 9 ciki a Tsholotsho.

An kama mahaifin yarinyar mai shekaru 29 a ranar 29 ga Oktoba 2022, jim kadan bayan an gano cewa ‘yarsa na da ciki. An bayyana cewa yana taimakawa ‘yan sanda wajen gudanar da bincikensu.

Mutane da yawa sun yi zargin cewa mahaifin yarinyar shine yaiwa ‘yarsa ‘yar shekara 9 fyade har ta samu juna biyu, wacce aka gano tana da wata kwayar halitta da ba kasafai ake samu ga yara masu shekarunta ba. 

Related Posts
1 of 407


Cibiyar Gwajin Kwayoyin Halitta (AGTC) ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kasa (Nust) ta ba da gudummawa don taimakawa hukumomi su gano wadanda suka ci zarafin yarinyar mai shekaru 9 da haihuwa. 

Sai dai sakamakon gwajin kwayar halitta ya tabbatar da cewa dan uwanta mai shekaru 13 da haihuwa shi ne yaiwa yarinyar ciki. 

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan kasar, Paul Nyathi, ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar; 

“’Yan sandan Jamhuriyar Zimbabwe sun tabbatar da cewa sakamakon gwajin kwayar halitta da aka samu daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kasa a ranar 25 ga Nuwamba, 2022, dangane da mahaifin yarinyar ‘yar shekara 9, ya tabbatar da cewa dan uwanta  mai shekara (13) ) shine ya dirka mata cikin.”

 “Yanzu haka dai ‘yan sanda suna aiki tare da sauran hukumomin gwamnati don ganin an bi hanyoyin da suka dace na doka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy